Hakkin mallakar hoto Dyson

Gwamnati ta sayi dubban na'urar taya marasa lafiya numfashi wato 'ventilator' don taimaka wa asibitoci wajen yaki da annobar coronavirus.

Ga marasa lafiyar da ke cikin mawuyacin hali, ventilator na taimakawa matuka gaya.

Mene ne ventilator kuma me ya ke yi?

A saukake, ventilator na maye gurbin yadda mutum ke numfashi idan cuta ta hana huhu aikinsa.

Wannan na bai wa jikin marar lafiya damar yaki da cutar har sai ya samu sauki.

Akwai nau'ikan ventilator da dama da ake iya mafani da su.

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, kashi 80 cikin dari na mutanen da ke fama da Covid-19 na samun sauki ba tare da an kai su asibiti ba.

Amma mutum daya cikin 6 na wadanda cutar ke kamawa na shiga mawuyacin hali kuma su kasa numfashi.

Idan haka ta faru, cutar na yi wa huhu illa. Garkuwar jiki na saurin gane haka kuma sai ta kara wa jijiyoyi girma don kwayoyin halitta masu dauke da sinadarin kare garkuwar jiki, su shiga cikin jijiyoyin.

Amma wannan kan ja ruwan ciwo ya shiga cikin huhu, kuma wannan kan sa yin numfashi ya yi wahala, sai yawan sinadarin oxygen (da ke taimakawa wajen numfashi) da ke jikin marar lafiyar ya yi kasa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

Amma a bangaren bayar da kulawa ta musamman wato ICU, ana saurin yi wa mai jinya amfani da na'urorin taimakawa wajen numfashi don tabbatar da cewa yawan sinadarin oxygen da ke jikin mutum ya na matakin da ya kamata.

Dakta Shondipon Laha, na Kungiyar Kula ta Musamman ya shaida wa BBC cewa mafi yawan masu jinya da ke fama da Covid-19 ba za su bukaci amfani da na'urar ventilator ba kuma suna iya yin jinyarsu a gida ba tare da zuwa asibiti ko kuma samun karin oxygen ba.

Amma duk da cewa akwai barazana idan ana amfani da ventilator, kamar rashin sanin wanda za ta yi wa illa nan gaba, ya ce, wani lokaci na'urar ventilator ce "kawai hanyar shigar da oxygen jikin marar lafiya".

Wani batu da dakta Laha ya yi bayani a kai shi ne, samun isassun ma'aikatan da za su iya sarrafa ventilator din.

"Na'urar ventilator na da wuyar sha'ani- tana iya janyo wa mai jinya illa idan ba a sarrafa ta yadda ya kamata ba," a cewarsa.

"Akwai ventilator iri-iri kuma wasu basu iya amfani da wani samfurin ba, don haka dole sai an taimaka masu idan ba su iya ba."

Hakkin mallakar hoto Intersurgical

Don shawo kan wannan matsalar, injin ventilator na taimakawa wajen tura iska mai dauke da sinadarin oxygen mai yawa cikin huhu.

Na'urar ventilator na da wata karamar na'ura mai sakin danshi, wanda yake dacewa da yanayin jikin marar lafiya.

Ana bai wa marar lafiyar magungunan da suke sa huhu da makogwaro da hanyar iska da ke jikinsa su rage aikin da suke yi don injin ventilator din ya yi duka aikin numfashin da ya kamata su yi.

Mutanen da cutar ba ta kama sosai ba na iya samun taimako ta bangaren numfashi wajen amfani da takunkumin fuska ko na hanci ko kuma wani dan bututu duk da ke aika iska zuwa huhu.

Injiniyoyi a Kwalejin Jami'ar landan, UCL, sun yi aiki da likitoci a asibitin koyarwa na jami'ar da kamfanin Mercedes formula One wajen gina wata na'ura da ake kira Continuos Positive Airway Pressure ko CPAP. Ana gwaji da ita a asibitoci da yawa a Landan kuma idan komai ya tafi dai-dai, kamfanin Mercedes-AMG-HPP zai fara samar da na'urorin guda 1,000 ko wace rana daga makon gobe (6 ga watan Afrilu).

Na'urar CPAP ta riga ta samu amincewar Hukumar kula da magunguna da kayayyakin kiwon lafiya ta Burtaniya.

Rahotannin farko-farko daga Lombardy da ke arewacin Italiya sun nuna cewa kusan kashi 50 cikin dari na marasa lafiyar da aka yi wa amfani da na'urar CPAP sun gujewa fadawa mawuyacin hali musamman ma amfani da na'urar ventilator.

Sai dai amfani da na'urar CPAP a marasa lafiyan da ke da cutukan numfashi da ake iya dauka ya janyo damuwa, saboda ko yaya aka samu kafar da iska za ta iya fitowa daga takunkumim, ma'aikatan lafiyar da ke kula da mai jinyar na iya kamuwa.

Na'urar ventilator nawa Burtaniya ke da shi- kuma nawa take bukata?

Insorar Lafiya ta NHS ta ce tana da na'urori guda 8,175 kuma ta na gaggawar bukatar sayen kari.

Gwamnati na ganin cewa ana bukatar kusan karin 30,000 a yayin da annobar ta kai ta kawo- kuma ta sayi guda 10,000 daga kamfanin fasaha na Dyson.

Wata majiya a kamfanin Dyson ta shaida wa BBC cewa sun yi sabon samfuri kuma an gwada shi a jikin dan Adam, yana aiki sosai.

Za a kuma sayen wasu 5,000 daga kamfanin Smiths group, a samfurinsa na ParaPac.

Wani kamfanin Burtaniya, Gtech ya kirkiri wani samfurin wanda zai iya aiki da sinadarin oxygen da ke asibitin amma ba tare da wutar lantarki ba.

Wasu kamfanonin - kamar Airbus da meggit da GKn - na kokarin samar da ventilator daga samfurin da ake da su a baya.

Yanzu dai, wata tawagar masana kimiyya da injiniyoyi daga Jami'ar Oxford da Kwalejin King's da ke Landan sun gabatar da sabon samfurinsu mai saukin kudi, wanda ta ce za a iya samar da shi cikin gaggawa.

Kuma masu bincike a Jami'ar East Anglia na duba yiwuwar amfani da magurzar tirdi wato 3D printing don gaggauta samar da wasu bangarori na na'urar ventilator tare da takunkumin fuska da sauran kayan amfani na asibiti.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Ventilator domin masu coronavirus